fidelitybank

Wani jigo a PDP ya sauya sheka zuwa APC

Date:

Gabanin zaben 2023, Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga daya daga cikin jiga-jigan dattijan jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Bojo-Bodinga ya samu tarba daga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Sanata Aliyu Wamakko (APC-Sokoto ta Arewa), a gidansa da ke Sokoto ranar Juma’a.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Sokoto ranar Asabar ta hannun mai ba da shawara ta musamman kan sabbin kafafen yada labarai na Wamakko, Bashar Abubakar.

Abubakar ya bayyana cewa taron ya samu halartan taron ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Ahmad Aliyu, da sauran fitattun ‘yan jam’iyyar APC da dama.

Ya ruwaito Alhaji Isa Sadiq-Achida, shugaban jam’iyyar APC na jihar a lokacin da yake magana a madadin jam’iyyar yana tabbatar wa sabon dan jam’iyyar da magoya bayansa cewa za su yi daidai da sauran mambobin jam’iyyar.

Ya ce, “Hakika ina da yakinin cewa sauya sheka na Bojo-Bodinga, alama ce mai kyau ga jam’iyyar APC kuma alama ce ta nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.”

A nasa bangaren, Bojo-Bodinga, dan jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Sokoto ta Kudu, ya bayyana cewa shi da jiga-jigan magoya bayansa a fadin jihar sun fice daga PDP zuwa APC.

punch newspaper headlines today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp