Wani Injiniya mai suna Anthony Usihe mai shekaru 37 ya mutu, bayan da ya makale a cikin tankin dizal da ke hanyar BUK a Kofar Dan Agundi a karamar hukumar birni a jihar Kano.
Da yake bayyana lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce, sun samu kiran gaggawa daga wani Sajan Salisu Inuwa na rundunar ‘yan sanda ta Sharada, inda aka yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka gano cewa, wani mutum ya makale a cikin tankin man na dizal.
Yusif ya ce an gano injiniyan a sume a cikin tankin diesel na injin janareta da ke ba da wutar lantarki ga eriyar sabis, amma daga baya ya mutu.
Ya ce an fara bincike don bankado sirrin da ke tattare da faruwar lamarin, domin babu wanda ya yi ikirarin ya ga mutumin kafin faruwar lamarin, inda ya ce, “an mika gawarsa ga Sajan Salisu Inuwa na sashin ‘yan sanda na Sharada.”