Wani matashi mai suna Musa David dan shekara ashirin da biyar a duniya mai karatu a Sashen Banki da Kudi na Waziri Umaru Federal Polytechnic (WUFP) a Birnin Kebbi ya kashe kansa.
David ya kashe kansa ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC a Birnin Kebbi.
Sai dai hukumar NSCDC ta musanta wannan zargi, wanda ya yi ta yawo a babban birnin jihar jiya.
Kakakin NSCDC, Akeem Adeyemi, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya ce, wannan rashin da’a da David ya yi ne ya tilasta wa Antinsa, Mrs Augustina Galadima, wacce ke zaune a gidan kwanan dalibai na Gangare, da ke Badariya, cikin birnin Birnin Kebbi, ta nemi taimakon wani jami’in NSCDC, wanda ake zargin ya kai shi ofishin hukumar domin tsira.
Ya gargadi jama’a game da illolin yada jita-jita tare da shawarce su da su rika tantance al’amura kafin su raba wa wasu.
Tuni dai aka mika gawarsa ga ‘yan uwansa domin yi musu jana’iza.