An samu tashin hankali a karamar hukumar Imeko Afon ta jihar Ogun, yayin da wani dalibi mai suna Ariyo Monday ya rasu bayan da wani malami ya yi masa bulala tare da neman ya yi tsallen kwadi 162.
Ariyo, dalibin makarantar Obafemi Grammar School, ya rasu ranar Juma’a.
Kamar yadda wani faifan bidiyo da wani mai fafutuka, Justadetoun ya wallafa a yanar gizo, ya bayyana cewa malamin ya dauki kwandon shara ya je ajin Ariyo ya ce wa daliban kada su fasa, amma marigayin cikin zolaya ya amsa wa malamin da wasa, inda ya ce an sayo kwandon da kudin daliban.
Ta bayyana cewa martanin da ya bayar ya bata wa malamin rai, inda ya kai kara ga shugaban makarantar kuma aka ba shi umarnin hukunta marigayin.
Justadetoun ya bayyana cewa, an yi wa Ariyo bulala 164 na sandar, kuma ana cikin haka sai ya fadi kasa.
Rahotanni daga faifan bidiyon cewa Ariyo da aka dora a kan drip tana nishi tana ta faman magana daga kan gadon asibiti.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Juma’a, ya ce sabanin rahotan, an yi wa marigayin dukan tsiya da sara 24, inda aka yi ta tsallen kwadi 162.
Odutola ya ce ya rasu ne a cibiyar lafiya ta tarayya dake Abeokuta.
Ta ce, “Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Oktoba, 2024. An bukaci marigayin ya yi tsallen kwadi 162, kuma an yi masa bulala 24 na rake. An garzaya da shi FMC Idi-Aba domin kula da lafiyarsa, kuma ya rasu yau (Juma’a).
PRO ya bayyana cewa an ajiye gawar a dakin ajiyar gawarwaki na Ayetoro domin a tantance gawarwakin kuma har yanzu ana ci gaba da binciken musabbabin mutuwar.