Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi watsi da yiwuwar samun wanda ya fi so a zaben shugaban kasa a 2023.
Buhari ya ce, ba shi da dan takarar da ya fi so a zaben shugaban kasa a 2023.
Ya yi alkawarin mika mulki ga duk wanda ‘yan Najeriya suka zaba a matsayin wanda zai gaje shi a 2023.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida, bayan kammala Sallar Eid-el-Fitr a Abuja.
Buhari ya ce, ba shi da dan takara na musamman da zai maye gurbinsa a badi.
Maimakon haka, shugaban ya ce, wanda zai gaje shi shine “mutumin da ‘yan Najeriya suka zaba”.