Aminu Abdulmumini Jor, mai sana’ar sayar da takalma mai shekaru 30, wanda rahotanni suka ce, ya yi tattaki mai nisan mil 808 daga jihar Gombe zuwa jihar Legas a kafa, domin nuna goyon baya ga muradin shugaban kasa na Bola Tinubu.
A cewar jaridar Sun, babban mai goyon bayan jigo a jamâiyyar APC ya ce, bai ji takaici ba duk da cewa, bai samu damar ganawa da shi ba.
Sai dai kuma kwanaki 25 da isar Legas Jor a yanzu ya makale kuma ba zai iya komawa gida ba.
Da yake magana da jaridar, Jor ya karfafa soyayyar da yake yiwa Tinubu duk da halin da yake ciki.
Ya bayyana cewa Tinubu ya taka rawa sosai wajen fitowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 2015.