Wani da ake zargin ya tsere daga gidan yarin Imo mai suna Mista Justice Anukam, a ranar Lahadi ya daba wa wata mata mai ciki wuka har lahira.
Lamarin ya faru ne a unguwar Umuejechi Nekede mai cin gashin kanta da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo.
A lokacin gabatar da wannan rahoto, matar da ba a san sunanta ba, an ce ‘yar asalin karamar hukumar Ohaji/Egbema ce ta jihar Imo.
Wani ganau cewa, rikicin ya fara ne a lokacin da wadanda ake zargin suka kama wadda ake zargin tana dawowa daga cocin inda suka nemi kudi a hannunta kuma matar ta ki amincewa kafin ka san wanda ake zargin ya dabawa matar wuka ne ta fadi har ta mutu har lahira. In ji Vanguard.