fidelitybank

Wanda ya aikata laifi aka ce ya mutu ya sake shiga hannu a Scotland

Date:

Kotu ta yanke hukuncin cewa wani mutum da aka kama a wani asibiti a Scotland a bara, dan kasar Amurka ne mai suna Nicholas Rossi, bayan an kammala bincike. Mutumin ya yi iƙirarin cewa shi ne wanda aka yi masa kuskure, kuma ya dage cewa sunansa, Arthur Knight mai makon Nicholas Rossi.
Amma Kotun Edinburgh Sheriff shaidar yatsansa sun yi daidai da na Rossi.
Hukumomi a Amurka na neman a tasa keyar Rossi, bisa zargin fyade da cin zarafi. Ana zargin cewa ya yi karyar mutuwar na sa ne kuma daga baya ya gudu zuwa kasar Scotland, domin gujewa fuskantar tuhuma.
Ya shafe shekara guda a matsayin sunan shi Arthur Knight, kuma shi maraya ne daga Ireland wanda bai taba zuwa Amurka ba.

A dai watan Maris mai zuwa ne kotun za ta yanke hukuncin cewa za ta mika mutumin zuwa Amurka ya fuskanci hukunci ko akasin haka. A shekarar da ta gabata ne dai ‘yan sandan Scotland suka kama Rossi a wani asibiti bayan da aka gano zanen da yake a jikin hannun sa na Tatto ya yi kama da nasa a lokacin da ake bashi kulawa a asibitin bayan ya sha fama da cutar Covid 19.
Sai dai a gwajin shaidar zanen ya tsayar sa ta yi daidai da wanda ake tuhuma, kamar yadda kwararriyar mai bincike Lisa Davidson ta shaidawa kotu.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp