Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos a Filato ya ce, mutum 148 aka kashe a hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jajiberin kirsimeti a yankin.
Hakan in ji jaridar Vanguard, na zuwa daidai lokacin da adadin mutanen da suka mutu sanadin hare-haren a ƙananan hukumomi uku na jihar ya kai 195.
Daga cikin adadin, an kashe mutum 148 a ƙaramar hukumar Bokkos dai 19 a ƙaramar hukumar Mangu da wasu 27 a Barkin Ladi.
An kuma ƙona gidaje 1,290 a Bokkos sai gida ɗaya a Mangu da shi ma aka ƙona sai dai har yanzu ba a kai ga sanin yawan gidajen da aka ƙona ba a Barkin Ladi.
Fiye da mutum 10,000 ne suka ɗaiɗaita sakamakon hare-haren na ƴan bindiga a yankunan Bokkos da Barkin Ladi.


