Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, ‘yan takarar da suka kasa amincewa da shan kaye a zaben da ya gabat,a ba su cancanci farin cikin samun nasara ba idan suka yi nasara a zabukan da ke gaba.
Shugaban, wanda ya bayyana hakan a gidan rediyon ranar Dimokuradiyyar kasar, ya amince cewa zaben shugaban kasa na 2023 ya yi zafi sosai, yana mai alakanta sakamakon da dimokuradiyyar kasar ke samu.
A cewar Bola Tinubu, “Kyawun dimokuradiyya shi ne wanda ya ci zabe a yau zai iya faduwa gobe, wanda kuma ya fadi yau zai samu damar yin takara da nasara a zagaye na gaba.”
Ya yi nuni da cewa wadanda ba su amince da sakamakon zaben ba a halin yanzu “suna cin gajiyar tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar don neman hakkinsu a gaban kotu kuma hakan na daya daga cikin dalilan da ya sa har yanzu dimokuradiyya ta kasance mafi kyawun tsarin gwamnati da mutum ya kirkira”.
Shugaban ya bayyana a matsayin dabi’a irin takaicin da ‘yan siyasar da sakamakon zaben da aka yi a watan Fabrairu da Maris bai amince da su ba.