Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, a ranar Juma’a, ya yi tir da harin da aka kai a cocin Fadan Kamatan, cocin Katolika na Kafanchan, da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Wani malamin darikar Katolika mai suna Naam Ngofe Danladi ya kone kurmus a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a gidan shugaban cocin Katolika na Kafanchan da ke Fadan Kamatan a Zangon Kataf ranar Alhamis.
Gwamna Sani da yake bayyana takaicinsa kan kashe-kashen, ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da tabbatar da cewa sun fuskanci fushin doka.
Muhammad Lawal Shehu, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an kai harin ne da nufin kunna wutar rikicin kabilanci da addini a Jihar Kaduna da kuma zagon kasa ga kokarin gwamnati na sake gina amana a cikin al’ummarta.
A cewar Gwamnan, “Na yi matukar bakin ciki da harin da aka kai a Fadan Kamatan Parish, Zangon Kataf.
“Wannan ta’addancin da ake yi wa masu bautar da ba su ji ba ba su gani ba, ba wai hari ne kawai ga al’ummar Katolika ba, a’a wani yunkuri ne na tayar da mutanenmu gaba da juna. Ba za mu amince da irin wannan ta’asa ba, kuma za mu yi iyakacin kokari wajen ganin an gurfanar da wadanda suka kai harin.”
Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta binciki lamarin tare da tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata laifin tare da fuskantar fushin doka.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ta dauki matakan da suka dace don dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ke fama da rikici ta hanyar karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro tare da sake farfado da hukumar ta Kaduna Vigilance Service (KADVS).
Hakazalika shugaban karamar hukumar Zangon Kataf Francis Sani ya bayyana alhininsa kan lamarin.


