fidelitybank

Wanda ake zargi da sayar da ‘Ya’yan sa uku ya shiga hannu

Date:

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Rivers, ta kama wani mutum bisa zarginsa da sayar da ‘ya’yansa guda uku.

Yayin da ‘yan sanda ke holen mutumin a ofishinsu da ke unguwar tsohuwar GRA a jihar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Grace Iringe-Koko, ta ce sun kama mutane masu yawa da ke harkar sayar da Æ™anana yara a fadin jihar.

Mutumin mai suna Michael Charles, ya amince cewa ya sayar da ‘ya’yansa, yana mai cewa talauci da rashin halin É—aukar nauyin ‘ya’yan nasa ne ya sanya shi É—aukar matakin.

Sauran mutanen da ke da hannu wajen sayar da yaran sun hadar da wani likita da kuma wani tsohon kansila.

Yayin da take magana a madadin mahaifiyar yaran wadda ita kurma ce, kakar yaran ta ce surukin nata ya daÉ—e yana sayar da ‘ya’yan da ‘yar tata ke haifa, tare da yi mata Æ™aryar cewa yaran mutuwa suke yi a lokacin haihuwarsu a asibiti.

Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, na cewa bayanan da suka samu sakamakon kama wasu da ake zargi da safarar Æ™ananan yara ne ya kai su ga gano waÉ—annan mutane, tare da mutanen da ke sayen jariran.

Bayan da ka kama su ne suka shaida wa ‘yan sanda yadda suka yi cinikin yaran.

”Daya daga cikin wadda ta sayi jariran mai suna Favour Amaewhule ta ce ta sayi jaririn a kan kuÉ—i naira 700,000, inda aka bai wa mahaifin jaririn naira 350,000, sauran 350,000 É—inn kuwa aka bayar da su ga tsohon kansilan tare da abokan hulÉ—arsa”, kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta bayyana.

A halin da ake ciki dai rundunar ‘yan sandan ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano Æ™arin mutanen da ke wannan mummunar sana’a, domin daukar mataki a kan su.

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp