A yau ne ake sa ran gurfanar da ɗalibin jami’ar da ya soki uwargidan shugaban Nijeriya, inda jami’an tsaro ke tsare da shi tsawon kwana 13 ba tare da shari’ah ba.
Zuwa yanzu babu masaniya a kan tuhume-tuhumen da hukumomi za su yi wa Aminu Adamu Mohammed, wanda aka yi zargin jami’an tsaro sun ɗauko shi ba tare da sanin hukumomin jami’arsa ba, kan umarnin Aisha Buhari.
Wannan mataki yana zuwa ne yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen a saki Aminu.
Ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam na ƙasashen duniya irin su Amnesty International, na ci gaba da matsa lambar cewa tsare Aminu Adamu cikin sirri ba tare da an kai shi kotu ba, abu ne da ya saɓa wa doka.
Ƙanin baban Aminu Baba Azare ya ce bayan tsare Aminu tsawon kwana 13, a ƙarshe hukumomi sun shaida musu cewa yau za a gurfanar da ɗan nasu gaban wata kotu a Abuja.
Ya ce suna fatan ganin an sake shi don ya je ya tunkari jarrabawarsa ta kammala jami’a da za a fara a makarantarsu.