Wakilai daga ƙasashe 80 da kungiyoyin ƙasashen duniya za su gana a birnin Paris nan gaba a yau domin tattauna hanyoyin kai agajin jin kai ga mutanen Gaza.
Taron wanda gwamnatin Faransa ta dauki nauyin shiryawa, ya mayar da hankali kan maido da muhimman kayayyaki kamar ruwa da man fetur da wutar lantarki tare da tabbatar da cewa agaji ya isa ga waɗanda ake so ba ƙungiyar Hamas ba.
Tawagogin ƙasashen Larabawa, da hukumar Falasɗinawa da Masar da wasu shugabannin Tarayyar Turai za su halarci taron.
Amma ba za a wakilta Isra’ila ba kuma Amurka tana tura tawagar masu ƙaramin karfi ne kawai.
Jami’an Faransa sun ce za a sanar da Isra’ila abubuwan da ke faruwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a makon da ya gabata ana buƙatar wasu dala biliyan 1.2 don biyan buƙatun mutanen Gaza da gaɓar yamma da Kogin Jordan.