Bayan kwashe tsawon watanni ana gwabza, a yau wakilai sama da 5,000 daga sassan Najeriya za su hallara a dandalin Eagle Square da ke Abuja, domin amincewa da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai aka kammala yarjejeniyar Abdullahi Adamu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira gwamnonin jam’iyyar 22 da suka yi taro tare da zartar da amincewar ‘yan takarar da aka amince da su a dukkan ofisoshin kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC). Daga nan sai ya zabi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kamar yadda ya faru a daren jiya, duk masu neman kujerar shugaban, sun janye daga takarar bisa ga umarnin Buhari.
Ba a yanke shawarar na sauran mukaman NWC na jam’iyyar bayan ganawar gwamnonin da Buhari. Shugaban ya ce, gwamnonin su hadu su amince a kan haka; cewa za a mayar da kudaden da aka kashe wajen siyan fom ga duk masu sha’awa
Abin takaici, kamar yadda ya faru a daren jiya, sa’o’i kadan kafin a fara kada kuri’a, gwamnonin sun kasa cimma matsaya kan kundin tsarin mulkin. Don haka, ba a aika jerin sunayen ba.
Daya daga cikin mukaman da har yanzu ake takaddama a kai shi ne na Sakataren jam’iyyar na kasa. Wasu gwamnonin na son Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, yayin da wasu ke neman Ifeoluwa Oyedele, dan takarar gwamna a jam’iyyar a jihar Ondo a 2020.