fidelitybank

Wakilai 811 za su zabi dan takarar shugaban kasa a PDP

Date:

Yanzu ya tabbata wakilai 811 ne za su yanke hukunci kan makomar masu neman shugabancin jam’iyyar PDP a babban taronta na kasa da za a gudanar a ranakun 28 da 29 ga watan Mayu.

Wakilai 811 na jam’iyyar sun kunshi wakilai na kasa daya da aka zaba daga kowace karamar hukuma 774 da kuma wakilai na musamman a kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja daga cikin nakasassu.

Hakan dai ya samo asali ne daga kin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabuwar dokar zabe wadda ta sauya sashe na 84 karamin sashe na 8, wanda majalisar dokokin kasar ta yi wa kwaskwarima da shigar da wakilai bisa doka cikin mahalarta taron da taron jam’iyyun siyasa.

Tun da farko dai jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zababbun wakilai ne kawai za su shiga zaben fitar da gwani na jam’iyyar a zaben fitar da gwani na jam’iyyar a babban zabe kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.

Tuni dai masu sha’awar neman zabe daban-daban suka rika zagawa cikin kasar domin neman wakilan da za su zabe su.

Jam’iyyar ta wanke tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsofaffin shugabannin majalisar dattawa, Bukola Saraki da Pius Anyim; tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi; Gwamnonin jihohin Bauchi da Sokoto, Bala Mohammed da Aminu Tambuwal domin neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sauran sun hada da; Gwamnan jihar River, Nyesom Wike; tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen; Masanin harhada magunguna, Sam Ohabunwa, gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, da dai sauransu. In ji Sahara Repoters.

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp