Mutumin da ya so yi wa jam’iyar PDP takarar gwamna a Jihar Kaduna a zaben 2023, Sanata Shehu Sani, ya ce, wakilai biyu ne suka zabe shi, kuma ko sisi bai ba su ba.
Sanata Sani ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.
A cewarsa, “Bai san wadanda suka zabe ni ba, wakilai kusan 300 ne suka kira ni suna ce min sune mutum biyun da suka zabe ni.
Ya taya Honorabul Isah Ashiru, mutumin da ya lashe zaben.