Wata mata da ake tuhumarta da kashe wani ɗan kasuwa ta lashe gasar mace mafi kyau ta “Miss Cell 2022”, a gidan gyara hali na Kirikiri da ke birnin Legas.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, matar mai suna Chidinma Ojukwu, wacce labarinta ya karade gidajen jaridu ba ta amsa laifin kisan kan da ake tuhumarta da aikatawa ba.
An dai kashe mutumin ne mai suna, Usifo Ataga a watan Yunin bara, wanda shi ne mamallaki tashar talabijin ta Super TV yayin da yake raye, bayan an daba ma sa wuka.
An ga hotunan Mis Ojukwu sanye da kayan da ake saka wa sarauniyar kyawun yayin da aka gudanar da bikin a cikin gidan gyara halin na Kirikiri, wanda shugaban hukumar gidajen gyara halin na ƙasa ya ce, ya na cikin abubuwan da suka shirya, domin bikin Ranar Mata ta duniya ta bana.