fidelitybank

Wadanda muka zalunta su yafe mana – Maryam Abacha

Date:

Maryam Sani Abacha, uwargidan tsohon shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha, ta yi Allah wadai da karuwar kalubalen tsaro da ke addabar kasar.

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta koka kan lamarin a wajen bikin cikarta shekaru 75 da haihuwa da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Hajiya Maryam ta yi amfani da wannan damar wajen addu’ar zaman lafiya, hadin kai, bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasa.

Sai dai ta yi kira ga shugabanni da daukacin al’ummar kasar da su ji tsoron Allah a duk harkokinsu. In ji Solacebase.

“Idan kowa zai ba da gudummawar kasonsa kuma ya zama dan kasa nagari, Najeriya za ta kasance kasa mai girma da wadata, in ji ta.

Maryam Abacha ta ce, ta yafewa duk wadanda suka yi wa iyali laifi ta wata hanya ko kuma ta daban, yayin da ta yi kira ga jama’a da su rungumi yafewa juna kuma su kasance masu rikon juna.

Ta ce, “Daya daga cikin abubuwan alheri a rayuwa shi ne mutane su rungumi ruhin gafara a tsakaninsu. Ya kamata mutane su koyi yadda ake gafarta wa juna. Gafara yana da matuƙar mahimmanci kamar yadda aka jaddada shi a cikin harsuna da addinai daban-daban. Yin afuwa yana inganta zaman lafiya tare da sauran fa’idodi,”

Maryam ta ci gaba da cewa, “Ina so in yi amfani da wannan dama wajen sanar da duk wanda ke nan da wanda ba ya nan cewa, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki kan duk abin da ya same mu na alheri ko mara kyau. Ina kuma son kowa ya sani na yafe wa wadanda suka zalunce mu, a lokaci guda, kuma ina son wadanda muka zalunta su yafe mana, domin Allah ya tsarkake zuciyata, kuma ina nan a raye ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki kan hakan. Zan iya mutuwa yanzu ko gobe, ina godiya ga Allah tsawon rayuwata.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp