Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce duk waɗanda ke da niyyar barin jam’iyyar adawa ta PDP gwamma sun fice tun yanzu domin bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta.
Saraki ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar alhamis inda ya mayar da martani bayan wasu jiga-jigan Jam’iyyar a jihar Delta sun sanar da ficewarsu a cikin makon nan.
A ranar Laraba ne Sheriff Oborevwori, gwamnan jihar ta Delta ya bar jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ke shirin komawa jam’iyya mai mulki nan ba da jimawa ba.
Oborevwori ya gaji Okowa a matsayin gwamnan Delta bayan ya lashe zaɓen 2023 a ƙarƙashin inuwar P D P.
Saraki ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama daga ƴan jam’iyyar da abin ya shafa da kuma matasa masu goyon bayan dimokraɗiyya game da rugujewar reshen jam’iyyar ta jihar Delta a kwanakin baya. “Waɗanda ke son barin PDP su bari tun yanzu, su bar sauran mu da ke son ci gaba mu mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar,” in ji sanarwar.
Saraki ya bayyana cewa adawa mai ƙarfi na da matukar muhimmanci ga ɗorewar dimokraɗiyya, inda ya ƙara da cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba a matsayin ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.
“Don ɗorewar dimokraɗiyya, dole ne a tabbatar da cewa mutane na da zaɓin da ya dace a kowane lokaci,” in ji shi.Wan