A yau ne za a kammala tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar ƙwadago, yayin da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC ke jiran matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka kan batun biyan mafi ƙarancin albashi na N250,000.
Shugabannin ƙwadagon sun jadadda cewa dole ne a kammala tattaunawar zuwa ranar Litinin, a yau kenan.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kammala taronsa, inda gwamnatin tarayya da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka cimma matsaya kan kuɗirin naira 62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
A halin da ake ciki dai a yanzu, ƙungiyayin ƙwadagon biyu sun dage a kan biyan mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata na naira 250,000.
Sai dai kungiyar gwamnonin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa duk wani mafi ƙarancin albashi da ya haura N60,000 ba zai ɗore ba.