fidelitybank

Waɗanda suka shigar da ƙorafin kirayen ga Natasha ba su bayyana kan su ba – INEC

Date:

Hukumar zaɓe INEC, ta bayyana cewa waɗanda suka tura koke da takardun sanya hannu kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye ba su sanya bayanan da ake buƙata ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da hukumar ta fitar a yau Talata, wanda ya samu sa hannun mai magana da yawun hukumar, Sam Olumekan.

Sanarwar ta ce “abin da hukumar ta lura da shi bayan kawo ƙorafin shi ne waɗanda suka jagoranci kawo ƙorafin ba su bayar da adireshi da lambobin waya da kuma adireshin tura saƙon email da za a iya tuntuɓar su ba”’.

“Adireshin kawai da aka rubuta a jikin takardar shi ne ‘Okene, jihar Kogi’, wanda wannan bai isa a iya tuntuɓar masu ƙorafin ba,” in ji sanarwar.

Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa “lambar wayar jagoran masu turo da koken ne kawai aka saka a wasiƙar, maimakon lambobin wayoyin dukkanin wakilan masu ƙorafin.”

A cikin sanarwar, INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.

Sanata Natasha Akpoti na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ta da shugaban majalisar dattijan Najeriya, Godswill Akpabio, bayan zargin da ta yi masa na yunƙurin cin zarafi na lalata.

Sai dai majalisar dattijan ta zargi Natasha da karya dokokin majalisa ta hanyar ƙin komawa sabuwar kujerar da aka sauya mata, da kuma yin hargowa a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisar na tsawon wata shida.

Yanzu haka dai hukumar zaɓen Najeriya ta tabbatar da cewa an kai mata ƙorafin neman yi wa ƴar majalisar kiranye, inda aka tura mata takardu ɗauke da sa hannun rabin masu kaɗa ƙuri’a 474,554 na rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓar ƴar majalisar a ƙananan hukumomin Adavi da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp