fidelitybank

Vinicius ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan FIFA

Date:

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior, ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo na Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) na shekara ta 2024.

Haka nan kuma Aitana Bonmati ta Barcelona ita ce ta lashe irin wannan kyautar a ɓangaren mata, karo na biyu a jere.

Vinicius ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan shekara, sai dai bai samu nasarar lashe ɗan wasa mafi ƙwazo ba a kyautar Ballon d’Or mai matuƙar farin jini.

An soki ƙungiyar Real Madrid saboda ƙaurace wa bikin bayar da kyautar ta Ballon d’Or.

Bonmati ta taimaka wa ƙungiyarta wajen lashe kofuna uku na cikin gida da kuma kofin zakarun nahiyar Turai na mata a kakar wasanni da ta gabata.

Haka nan ta zura ƙwallo a wasan kusa da na ƙarshe da kuma na ƙarshe lokacin da ƙasarta Sifaniya ta lashe gasar Nations League a watan Fabarairu.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp