fidelitybank

VeryDarkMan ya gabatar da hujjoji kan zargin Bobrisky da ba jami’an gwamnati cin hanci

Date:

Martins Vincent Otse da mutane suka fi sani da Verydarkman ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya da aka kafa domin yin bincike kan zarge-zargen cin hanci kan wasu jami’an hukumar kula da gidajen yari da na hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa.

A kwanan nan ne Verydarkman ya yi wata fallasa inda ya saki sautin muryar da ya ce ta Bobrisky ce da ke iƙirarin biyan wasu jami’an EFCC maƙudan kuɗi domin janye wasu tuhume-tuhume da ake masa inda kuma ya yi iƙirarin cewa bai zauna a gidan yari ba tsawon hukuncin aka yanke masa.

Wannan bankaɗa ta sa hukumomi kafa kwamiti domin gudanar da bincike lamarin da ya kai ga dakatar da wasu manyan jami’an hukumar kula da gidajen yari saboda zarginsu da hannu a lamarin.

Hukumar gudanarwar kula da gidajen yari da shige da fice da gobara ta Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da jami’an ne domin ba da sararin gudanar da bincike kan zargin da ake masu.

A ranar Litinin ne Verydarkman ya bayyana gaban kwamitin inda ya yi zargin cewa Bobrisky wanda asalin sunansa Idris Okuneye yana yi wa mutumin da ake zargin ya ba shi rancen kuɗi barazana.

Verydarkman ya gabatar da jawabinsa gaban kwamitin inda kuma ya gabatar da wasu takardu da a cewarsa hujjojinsa ke nan.

Ya yi iƙirarin cewa ya yaɗa sautin muryar a shafukan sada zumunta bayan da ya saurari sautin ya kuma ga cewa wasu jami’an EFCC suna da hannu a lamarin.

A cewar Verydarkman ya yi haka ne saboda barazanar da Bobrisky ke yi wa mutumin da ya ba shi rancen naira miliyan huɗu – “mutumin ya ba shi rance kuma da lokacin karɓar rancen ya yi, Bobrisky ya ƙi biyansa, ya kuma ɓuge da yi masa barazana,”.

“Abokina ne ya aiko da rasiti, Sai Bobrisky ya riƙa roƙon abokin nawa sannan ya biya amma da na saurari sautin, sai na ajiye shi.”

Tun farko Verydarkman ya shaida wa kwamitin cewa ba zai yi magana ba matuƙar Bobrisky da shugaban EFCC Ola Olukoyede ba su bayyana gaban kwamitin ba, sai dai daga baya ya yi magana bayan da kwamitin ya nemi Verydarkman ya yi bayani kan sautin da ya yaɗa ranar 23 ga Satumba wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta. In ji BBC.

latest nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp