Dan kwallon baya na Manchester United, Raphael Varane zai bar kulob din idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana.
Dan wasan mai shekaru 31, ya koma Old Trafford ne daga Real Madrid a bazarar 2021 a kan fan miliyan 34.
Varane ya buga wa United wasa sau 93.
Tsohon dan kwallon Faransa ya taimaka wa United lashe kofin Caraboa a 2023 lokacin da tawagar Erik ten Hag ta doke Newcastle United a wasan karshe.
“Kowa a United na godiya ga Rapha saboda aiki da yayi kuma muna masa fatan alheri a nan gaba,” in ji sanarwar United.