Gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Juma’a sun mika takardar tsayawa takarar shugaban kasa tare da bayyana bukatar shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan.
Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, shi ma ya mika fom din takararsa na shugaban kasa a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja.
Wata kungiya mai suna National Stability Project ta saya tare da gabatar da fom din takarar shugaban kasa ga shugaban majalisar dattawa a ranar Litinin da ta gabata, kuma ya karba.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama da suka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibajo da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne suka siya fom din wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 100.