A yau Laraba ne, ake jana’izar uwargidan tsohon gwamnan Kano, Hajiya Ladi Baƙo, bayan ta rasu a wani asibiti da ke cikin jihar.
A fadar Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu za a yi wa marigayigar mai shekara 93 salla, kafin a binne ta daga bisani.
‘Yar marigayiyar, kuma tsohuwar kwamishiniya a jihar Kano, Hajiya Zainab Audu Baƙo ce ta tabbatar da mutuwar cikin alhani lokacin zantawa da BBC Hausa ta wayar tarho.
Mijin marigayiyar, Kwamishinan ‘Yan sanda, Audu Baƙo ya jagoranci Kano a matsayin gwamna daga 1967 zuwa 1975.
Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin Kano da suka fi aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a jihar.