Matar shugaban Amurka Jill Biden ta kai ziyarar ba-zata a Ukraine yayin balaguron da take yi zuwa Romania da Slovakia, inda take jaddada goyon bayan Amurka ga ƙawayenta na Nato.
Mrs Biden ta gana da matar shugaban Ukraine Olena Zelenska a wata makaranta da ke garin Uzhhorod, wanda yanzu ake amfani da shi a matsayin wurin ɓuya ga fararen hula.
Uwar gidan Biden É—in ta ce ta so ne ta nuna cewa “Amurkawa na tare da jama’ar Ukraine”, inda ta Æ™ara da cewa yaÆ™in wanda yanzu ya shiga wata na uku “na rashin imani ne” kuma dole a dakatar da shi.
Mrs Zelenska ta ce abu ne “na bajinta” mutum ya ziyarci Ukraine.
“Mun fahimci irin haÉ—arin da mai É—akin Biden ta saka kanta a ziyarar da ta kawo Ukraine, lokacin da ake ta É“arin wuta a kowace rana, ake kunna jiniya kowace rana, har a yau,” in ji ta.