Wata mata ‘yar shekara 33 mai suna Olaide Adekunle ta sayar da jaririnta mai watanni 18 domin ta biya bashi a jihar Ogun.
Mahaifiyar wadda a halin yanzu tana hannun ‘yan sanda, ta sayar da jaririn ne a kan kudi Naira 600,000 ga wani mai saye da har yanzu ba a tantance ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa, an kama matar ne biyo bayan wani korafi da mijin matar, Nureni Rasaq ya shigar a sashin ‘yan sanda na Sango.
Mijin ya shaida wa ‘yan sanda cewa matarsa ta je Legas ne a ranar 15 ga Maris, 2023, tare da jaririyarsu Moridiyat Rasaq; yana mai cewa ta koma gida batare da jaririya ba.
Mista Rasaq ya kara da cewa matarsa ta ki yi masa magana kan inda yaron yake, duk da kokarin da ta yi na yin magana.
Dangane da rahoton, Oyeyemi ya bayyana cewa DPO na yankin Sango, CSP Dahiru Saleh, ya bayyana mutanensa da suka kama matar.
“Da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta sayar da jaririn ga wani a Legas a kan kudi N600,000,” in ji Oyeyemi.
Da aka tambaye shi, Oyeyemi ya ruwaito mutumin yana cewa, “ta ci bashin kudi ne daga bankin ‘yan kasuwa, kuma a lokacin da ta kasa biya kudin, sai jami’an bankin suka fara jan ta tare da yi mata barazanar cewa za su yi maganinta.”
Hakan yasa ta ruga da gudu zuwa Legas domin ta kwaso ruwan buhu.
A cikin harkar siyar da ruwan buhu ne ta hadu da wani mutum wanda ya gabatar da ita da wata mata wadda a karshe ta siyo yaron a Legas.
A halin da ake ciki kuma, mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, DCP Babakura Muhammed, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa hukumar CIID ta jihar domin ci gaba da bincike tare da yiwuwar dawo da jaririn.


