Uruguay da Italiya za su fafata a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 ta 2023 a wasan karshe da ake fafatawa a kasar Argentina.
Kungiyoyin biyu sun yi nasara a wasanninsu na dab da na karshe ranar Alhamis a Buenos Aires.
Uruguay ta lallasa kungiyar Isra’ila da ci 1-0 a gasar da aka yi a safiyar yau.
Simone Pafundi ya buga bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Italiya ta lallasa Koriya ta Kudu da ci 2-1.
Uruguay ko Italiya ba su taba lashe kofin ba a tarihinsu.
Isra’ila wadda ke buga gasar a karon farko, za ta buga wasan na uku ne a ranar Lahadi da Koriya ta Kudu.