Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta sake zaɓar Ursula Von der Leyen, a matsayin shugabar hukumar Tarayyar Turai.
Ms Von der Leyen za ta jagoranci hukumar har zuwa shekara biyar masu zuwa.
Da take jawabi bayan zaɓen, shugabar hukumar ta ce kare martabar dimokradiyyar Turai shi ne babban abin da za ta sanya gaba.
Ta ce ”muna aiki tare don karfafa nahiyar Turai, muna aiki a kan batutuwan da suka shafi ci gaba da gogayya a ciki tattalin arzikinmu”.
Fiye da mambobin Majalisar 400 daga cikin 720 ne suka zaɓi Ms von der Leyen ciki har da waɗanda suka fito daga ɓangaren masu son kawo sauyi da na ɓangaren masu matsakaicin sassaucin ra’ayi.
Ta dai yi alƙawarin bai wa EU babbar dama wajen kare kanta daga dukkan wasu ƙalubale musamman na tsaro, tare da tabbatar da cewa ƙasashe mambobin hukumar za su rage fitar da iskar da ke gurɓata muhalli da kashi 99 cikin 100 nan da 2040.