Gwamnatin jihar Nasarawa a kokarinta na magance matsalar jabun magunguna a jihar, ta hada gwiwa da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, domin yaki da yaduwar magungunan jabu a cibiyoyin kiwon lafiya na firamare da manyan makarantu a fadin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Gaza Gwamna ne ya sanar da hakan a yayin ziyarar duba da hukumar kula da magunguna da kayayyaki ta jihar Nasarawa (NASDMA) da ke Lafia babban birnin jihar a ranar Talata.
Gwamna ya bayyana cewa, ci gaba da inganta kayan aiki da suka hada da rumbun ajiya a NASDSMA, na da nufin tabbatar da gudanar da ingantattun magunguna da rarraba magunguna daidai da ka’idojin kasa da kasa.
Ya bayyana gamsuwa da ingancin aiki da kayayyakin da aka yi amfani da su wajen aikin, inda ya bayyana shi a matsayin mafi inganci a shiyyar Arewa ta Tsakiyar.
Kwamishinan ya ci gaba da bayyana muhimmancin hukumar wajen magance kalubalen samar da magunguna da kuma saukin kudi a cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a a fadin jihar.
Ya yabawa hukumar UNICEF bisa gagarumin gudunmawar da ta bayar wajen gudanar da aikin, inda ya bayyana cewa hakan na nuni da kudirin kungiyar na inganta harkokin kiwon lafiya a jihar Nasarawa.


