Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya yabawa gwamnatin tarayya da jamiāan tsaro kan ceto yaran da aka sace a jihar Ondo.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa, an ceto yaran da wasu manya daga wata coci.
Wata sanarwa da kwararre kan harkokin sadarwa na UNICEF, Geofery Njoku ya sanya wa hannu, ta ce, ba za a taba tsare yara ba tare da son ransu ba a kowane irin yanayi.
Ta yi Allah-wadai da cin zarafin yara, inda ta yi gargadin cewa ana auna alāumma ne da yadda take muāamala da āyaāyanta.
UNICEF ta kuma dorawa gwamnati alhakin kara kokarin kare yara daga kowane irin tashin hankali.
UNICEF ta yaba da yadda aka ceto kimanin yara 27 da aka yi garkuwa da su ba tare da son ransu ba a wani coci a jihar Ondo.