Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce umarnin da Isra’ila ta bayar na kwashe marasa lafiya a asibitoci fiye da 20 a arewacin Gaza daidai yake da hukuncin kisa ga mutanen da ke kwance asibitin suna jinya.
Hukumar ta yi nuni da mutanen da ke cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai ko kuma jariran da ke cikin kwalba.
Tuni asibitocin Gaza suka shiga cikin wani yanayi na tashin hankali da rudani.
Wata jami’ar WHO ta ce halin da Gaza ke ciki na da matuƙar tayar da hankali, dangane da ko mutum ya tsaya ko kuma ya fice, abin da muke gani shi ne yadda aka lalata yankin.
Likitoci sun shaida wa BBC cewa, ana ƙarancin magunguna a asibitocin sannan kuma man da ya rage musu da ake amfani da shi a injinansu bai taka kara ya karya ba.