Gabanin. zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, gwamna David Umahi, ya amince da kakakin majalisar dokokin jihar Francis Nwifuru a matsayin wanda ya fi so zai maye masa gurbi.
Umahi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar a Okposi da ke karamar hukumar Ohaozara a yayin bikin jana’izar marigayi Dandy Omoke wanda ya taba zama shugaban karamar hukumar.
Umahi, yayin da yake gabatar da shugaban majalisar a wurin taron, ya bayyana shi a matsayin gwamnan jihar.
Nwifuru, wanda ke wakiltar mazabar Izzi ta Yamma, ya kasance kakakin majalisar dokokin jihar Ebonyi tun a shekarar 2015.
A halin yanzu yana cika wa’adinsa na uku. A shekarar 2011 ne aka fara zabar sa a majalisa a karkashin jam’iyyar PDP.