Mutane uku ne suka rasa rayukansu a unguwar Obada da ke Abeokuta, jihar Ogun bayan wata babbar mota ta afkawa wata motar haya a safiyar Lahadi.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 07:15 na safe, bayan ofishin ‘yan sanda na Obada, a kan hanyar Legas zuwa Abeokuta ya kai ɗauki.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce manya maza biyar ne suka hadu da hatsarin.
“Mutane biyu sun sami raunuka kuma abin takaici, mutane uku sun mutu,” Okpe ya tabbatar.
Ta kara da cewa motocin da abin ya shafa sune karamar mota kirar Volvo wacce ba ta da lambar rajista da tasi, mota kirar Nissan mai lamba AKM489ZY.
“Abinda ake zargin ya haddasa hatsarin shine keta haddi daga bangaren direban babbar motar a lokacin da ya yi karo da motar Nissan.”
Rahotanni sun ce an kai wadanda suka jikkata zuwa wani babban asibiti da ke Abeokuta domin kula da lafiyarsu yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.
A halin da ake ciki, kwamandan hukumar FRSC reshen Ogun, Ahmed Umar, yayin da yake jajantawa iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su, ya shawarci masu ababen hawa da su guji keta hanya gaba daya.
Umar ya kara da cewa, tsaro aikin kowa ne, musamman a wannan lokacin da ake yawan zirga-zirgar ababen hawa, yana mai cewa, “Kowa ya kamata ya tuka mota cikin taka-tsantsan da bin ka’idojin zirga-zirga.”