fidelitybank

Ukraine za ta cigaba da fitar da kayan abinci zuwa kasashen Afrika

Date:

Ministan harkokin waje na Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce a shirye kasarsa take ta koma ta ci gaba da fitar da hatsi zuwa kasashen Afirka da sauran sassan duniya ba tare da wani sharadi ba, idan har Rasha ta kawo karshen rufe hanyar da ta yi ta teku ( Bahar Aswad).

A wata hira da jaridar kasar Tanzania ta, Citizen, ministan ya ce, duk da cewa kasashen Afirka da yawa sun kasance ‘yan ba-ruwanmu a yakin mamayar da Rasha ke yi da karasa, Ukraine za ta tabbatar da ci gaba da aiwatar da bangarenta na yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Ya ce, Ukraine, za ta ci gaba da aiki kut da kut tare da dukkanin kasashen Afirka a kwanaki da makonnin da ke tafe domin ta tabbatar dukkanin kayan abincin da aka saya sun kai ga kasuwannin kasashen.

Ta kuma yi kokarin kawo karshen karancin abincin da ake yi a duniya, wanda Rasha ta haifar, in ji shi.

Mista Kuleba ya bukaci duniya da kuma dukkanin kasashen Afirka da su yi aiki tare su matsa wa Rasha lamba ta bari a rika wucewa da kayan abinci ta ruwa zuwa kasashe.

Farashin mai da kayan abinci a Afirka ya yi tashin gwauron-zabi tun daga ranar 24 ga watan Fabrairu, lokacin da yakin Rasha da Ukraine ya barke.

Duk wani yunkuri na wasu shugabanni na sassauta lamarin wanda rikicin ya haddasa ya gagara samun nasara.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp