Ministan harkokin wajen Ukraine ya yabawa kungiyar tsaro ta NATO kan samun hadin-kai mai karfi da matakan da suke dauka wajen marawa kasarsa baya.
Dmytro Kuleba ya samu halartar taron ministocin ketaren kasashen Nato a Brussels.
Ya kuma bukaci a basu ƙarin makamai domin yaƙar sojojin Rasha da ke musu mamaya.
Kafin tattaunawar, Sakatare Janar na ƙungiyar ta Nato, Jens Stoltenberg ya ce, kungiyar za ta duba bukatar Ukraine na neman ƙarin makamai da taimakon soji domin kare kanta.
Ya ce “abubuwan da muka gani cikin kwanaki ya kazanta sosai a wannan yaki, don haka muke duba muhimmanci taimakawa Ukraine.
“Kuma ina ganin zuwan Mista Kuleba wannan wuri a yau na da muhimmanci sosai, domin mu tattauna kan yadda za a taimaka wa Ukraine na aiki da Nato amma ba ta cikin kungiyar.”