Shugaban sojojin Ukraine ya ce makamansu masu-linzami sun lalata jiragen ruwan Rasha guda biyu da ke sintiri a Bahar Aswad.
“Mun lalata jiragen ruwan Rasha biyu samufurin Raptor-class da safiyar nan kusa da Tsibirin Zmiinyi (Snake),” a cewar babban jami’in rundunar sojan Ukraine Valeriy Zaluzhniy.
Wasu bidiyo da rundunar sojin Ukraine ta fitar da ba a tantance su ba sun suna wasu abubuwa da ake tsammani makamai masu-linzami ne sun fada kan jiragen ruwan biyu a yayin da suke sintiri a kusa da Bahar Aswad
Kawo yanzu Moscow ba ta ce komai a kan batun ba.