Rundunar sojin saman Ukraine ta ce ta sake harbo wani jirgin saman Rasha Su-34, lokacin da jirgin ke ƙoƙarin harba bama-bamai a wasu yankunan ƙasar.
A cewar sojojin ƙasar ta Ukraine, sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Maris.
An ruwaito cewa wannan shi ne jirgin saman Rasha mai suna Su-34 na shida da sojojin Ukaraine suka kakkaɓo a makon nan.
Sojojin Ukraine ɗin sun yi iƙirarin cewa sun harbo jiragen yaƙin Rasha 13 a cikin makonni biyu a kacal a cikin watan Febrairu, sama da wanda suka yi a watannin baya na yaƙin.