Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce Ukraine ta kai wa jirgin ruwanta hari a birnin Kerch mai tashar ruwa da ke yankin Crimiea da ta mamaye.
Rashar ta ce a ranar Asabar Ukraine ta harba makamai masu linzami 15, amma dukansu sojinta sun kakkaɓo su, sai guda ɗayan nan da ya faɗa kan jirgin ruwan.
Tun da fari, sojin Ukraine sun wallafa a shafin Telegram cewa sun yi nasara a harin da suka kai birnin na Kerch.
Wani ɗan jarida mai goyon bayan Ukraine ya ce harin ya faɗa kan ƙaramin jirgin ruwan Rasha mai suna Askold, sai dai babu hoto ko bidiyon da ya tabbatar da bayanin nasa.