Jami’an tsaron Ukraine sun dauki alhakin kai wani harin bam da ya hallaka wani babban janar din sojin Rasha da ake zargi da amfani da makamai masu guba a Ukraine.
Laftanar janar Igor Kirillov, shi ne shugaban rundunar kula da makaman nukiliya da masu guba na Rasha.
Ɗaya daga cikin Yulia,mazauna yankin da abin ya fashe ta shaida wa BBC cewa “mun ji kara mai karfin gaske, na tsorata matuka, na kasa leka taga na ga abin da ke faruwa a waje. Sai karar motocin daukar marassa lafiya kawai ka ke ji, nan da nan wurin ya rude da koke-koke.”
A jiya litinin masu shigar da kara a Ukraine suka zargi Janar Kirillov da hannu a harin makamai masu guba kan sojin Ukraine.