Ukraine ta yaba wa karfin halin shugabannin Turai uku wadanda suka yi doguwar tafiya mai hadari ta jirgin kasa zuwa Poland domin nuna goyon bayansu yayin da birnin ke fuskantar karin hare-haren Rasha.
Firaministan Poland da na Slovenia da kuma na Jamhuriyar Czech ne suka gana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a ranar Talata da yamma yayin da dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a Kyiv.
Poland ce dai ta kirkiri wannan tafiya, bayan da Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan hadarin da ke tattare da yinta.
Firaministan Czech ya ce Ukraine na fada ne domin ‘yancinta. A cewar BBC.