Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce, kasarsa na bukatar sama da tallafin agaji na dala miliyan dari takwasi, domin tunkarar matsalar karancin makamashi da hare-haren bama-baman Rasha ya haddasa musu.
Galibin yankunan kasar sun kasance babu lantarki, yayin da ake gudanar da wani taron kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa, domin tattauna irin taimakon da za a iya bai wa Ukraine.
Shugaba Zelensky ya shaida wa wakilan taron cewa asibitoci da sauran wurare ba su da karfin ci gaba da amfani da injin janareta domin samun wutar lantarki.