fidelitybank

Uhuru Kanyatta zai jagoranci jami’an sanya ido a zaben Najeriya

Date:

Ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afirka, AU ta naɗa tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta domin ya jagoranci tawagar jami’anta da za su yi aikin sa ido a zaɓukan da ke tafe a Najeriya.

Tawagar masu sanya idon ta ƙunshi wakilan hukumoimin zaɓe na ƙasashen ƙungiyar ta AU da ƙungiyoyin farar hula da ƙwararru masu zaman kansu da kuma wasu hukumomi na ƙungiyar ta AU.

Aikin tawagar zai ƙunshi sanya ido tare da bayar da bayanai masu inganci a kan zaɓukan da kuma bayar da shawara kan yadda za a inganta zaɓen a nan gaba bisa abubuwan da suka gani.

Ana kuma sa ran tawagar ta nuna goyon bayanta da tallafa wa dorewar tsarin dumukuraɗiyya da zaman lafiya da ci-gaba a Najeriya.

A ranar 25 ga watan nan na Fabarairu ne ‘yan Najeriya za su yi zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisun dokoki na tarayya sannan kuma ranar 11 ga watan Maris su yi zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki na jiha.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp