Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, za ta ba da sanarwar kakaba takunkumin tattalin arziki a kan kungiyoyi goma a Turai, saboda rashin bin ka’idojin cinikin kudi a kakar wasa ta 2020/2021, ciki har da Barcelona da Paris Saint-Germain, in ji Times.
Lokacin da aka tabka kurakurai game da sarrafa tattalin arziki ya yi daidai da isowa da fashewar cutar ta COVID-19.
Binciken farko da UEFA ta yi ya nuna kungiyoyi kusan 20, wadanda suka hada da kulob din Arsenal na Premier da kuma Marseille ta Faransa.
Amma kamar yadda al’amura ke tafiya, har yanzu ba a shigar da asusun karshe na yawancin kungiyoyin 20 da UEFA ba, kuma da zarar an yi hakan, yanayinsu na iya canzawa.
Shari’ar irin su PSG, Barcelona, da Juventus, duk da haka, ya sha bamban sosai.
PSG da Barcelona sune kungiyoyin biyu da aka ce sun fi fuskantar hadari yayin da suke ci gaba da shari’a a kan UEFA tare da Real Madrid saboda batun Super League gaba daya.
A yanzu dai Barcelona da Juventus sun ki tattaunawa da UEFA.


