Mai gabatar da kara a Ukraine, ya bukaci gwamnatin Turkiyya ta tsare jirgin dakon kayan Rasha, wanda ta yi zargin ya na dauke da hatsin da suka sace daga daga birnin Berdyansk da ke tashar ruwan Baharul Aswad.
Shafin intanet na dakon kaya ya nuna jirgin Rashar mai suna Zhibek Zholy, yana tashar ruwan Karasu da ke Turkiyya wadda ke yammacin birnin Santambul.
Sai dai a baya-bayan nan Rasha ta musanta zargin na Ukraine, kan sace abinci nau’in hatsi a yankunan da sojinta suka yi wa kawanya.
A wani bangaren kuma sojin Rasha sun ci gaba da kai munanan hare-hare a birnin Lysychansk, wanda shi ne kaÉ—ai ke hannun sojin Ukraine a yankin Luhansk.
Shugaba Volodymyr Zelensky, ya kuma zargi Rasha da ayyukan ta’addanci, bayan harin makamai masu linzamin da ta kai da tsakar dare a birnin Odessa mai tashar ruwa da ya hallaka sama da mutum 20