Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya Ali Yerlikaya a ranar Juma’a ya ce, ‘yan sanda sun tsare wasu mutane takwas da ake zargi da sayar da bayanai ga hukumar leken asirin Isra’ila, Mossad.
Da yake bayyana hakan a dandalin sada zumunta na X, Yerlikaya ya ce an tsare biyu daga cikin wadanda ake zargin kuma an yanke hukuncin shari’a ga wasu shida.
Ya ce wadanda ake zargin sun yi taro da jami’an leken asirin Isra’ila tare da tattara bayanai kan daidaikun mutane da kamfanoni a Turkiye da Mossad ya kai wa hari.
Ya kara da cewa sun mika bayanan da takardu ga jami’an leken asirin Isra’ila.
An gudanar da samamen tare da hukumar leken asiri ta kasar Turkiyya a cewar ministan.
Bidiyon da ministan ya fitar ya nuna yadda ‘yan sanda ke kai wadanda ake zargi zuwa asibitin jihar domin duba lafiyarsu sannan kuma zuwa ginin ma’aikatar shari’a da ke Istanbul.
Yerlikaya ya ce “Ba za mu taba barin ayyukan leken asiri da aka yi niyya don cin karo da hadin kan kasa da hadin kanmu a cikin iyakokin kasarmu ba.”