Gwamnatin Turkiyya ta ce sojojinta sun kai hari maɓoyar mayaƙan ƙungiyar Kurɗawa ta PKK masu alaƙa da Iraƙi da Siriya, bayan da aka zarge su da kai wani hari kan masana’atar jiragen sama.
A ranar Laraba ne wasu mutane biyu mace da namiji suka buɗe wuta a kusa da mashigar masana’antar, mai nisan kilomita 40 daga wajen babban birnin ƙasar Ankara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata 22.
Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce harin da sojojin ƙasar suka kai moɓayar mayaƙan ƙungiyar ya lalata gine-gine 47 na ƙungiyar.
Shugaban ƙasar, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana hari kan masana’atar jiragen saman da ”abin taƙaici” a shafinsa na X.
Ministan tsaron cikin gida na ƙasar, Ali Yerlikaya ya ce ɗaya daga ckin maharan ɗan ƙungiyar PKK ne mai suna Ali Orek. In ji BBC.
Ƙungiyar Kurɗawa ta PKK, haramtacciyar ƙungiyar ce da aka bayyana da ta’addanci a Turkiyya da Amurka da Birtaniya, inda kuma take yaƙi da hukumomin Turkiyya tun shekarun 1980, kan abin da ta kira ƙwatar ‘yancin Kurɗawa marasa rinjaye a ƙasar.