fidelitybank

Turkiyya ta dakatar da hulɗar kasuwanci da Isra’ila

Date:

Turkiyya ta ce ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra’ila dangane da yaƙin da ake yi a Gaza, saboda taɓarɓarewar yanayin jin ƙai a yankin.

An dai yi ƙiyasin adadin cinikayyar tsakanin ƙasashen biyu ya kusan dala bilyan bakwai a bara.

Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Turkiyya ta ce za a aiwatar da matakin har sai Isra’ila ta bayar da damar shigar da kayan jin ƙai zuwa Gaza ba tare da matsala ba.

Kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ta kai kusan dala biliyan bakwai a shekarar da ta gabata.

Ministan harkokin wajen Isra’ila ya zargi shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da kasancewa kamar mai mulkin kama karya.

Israel Katz, a shafin X, ya ce Mista Erdogan yana burus da buƙatun al’ummar Turkiyya da na ƴan kasuwa da watsi da yarjeniyoyin kasuwanci tsakanin ƙasashen duniya.

Ya ƙara da cewa ya umarci ma’aikatar harkokin waje da ta samar da wasu hanyoyin kasuwanci da Turkiyya da nufin mayar da hankali kan samar da kayayyaki a cikin gida da kuma shigo da wasu kayayyaki daga wasu ƙasashe.

Cikin wata sanarwa, Turkiyya ta ce dakatar da hulɗar kasuwancin ta shafi duka kayayyaki.

A 1949, Turkiyya ce ƙasar da galibin al’ummarta musulmi ne ta amince da Isra’ila. Sai dai alaƙa tsakaninsu ta yi tsami a shekarun baya-bayan nan.

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp